
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na 28 a gasar Premier League a Emirates ranar Lahadi.
Palace za ta buga wasan karkashin kociyan matasanta ‘yan shekara 21, Paddy McCarthy, bayan da ta kori Patrick Vieira.
Albert Sambi Lokonga ba zai fuskanci kungiyarsa ba, yayin da ake auna koshin lafiyar Will Hughes da James McArthur, da kyar idan gola, Vicente Guaita zai yi karawar.
Mai tsaron bayan Arsenal, Takehiro Tomiyasu da kuma William Saliba an sauya su, wadanda suka ji rauni a karawa da Sporting a Europa League.
Wasa tsakanin kungiyoyin biyu:
Crystal Palace ta ci wasa biyu ne daga 22 da suka fuskanci juna a baya a lik,
Sai dai Arsenal ta barar da maki a wasa da Palace a gida a haduwa hudu baya da suka yi.
Asalin hoton, BBC Sport
Idan Gunners ta hada maki uku, za ta tara yawan wanda ta hada a bara 69 a lokacin da saura wasa 10 a karkare Premier League.
Ta ci wasa biyar a jere saura daya ta yi bajintar Newcastle Uniteda a bana, wadda ta yi hakan tsakanin Oktoba zuwa Disambar 2022.
Haka kuma za ta yi kan-kan-kan da cin wasa shida a jere a Premier karkashin Mikel Arteta.
Arsenal na fatan zama ta farko da ta ci wasa sama da takwas a karawar hamayya ta ‘yan birnin Landan a bana.
A wasa tara da ta buga a kakar nan karawa daya ce ta tashi 1-1 da Brentford a gida.
Palace, wadda yanzu ta yi wasa 11 a Premier League ba tare da yin nasara ba, ta taba buga 14 ba ta ci ko daya ba tsakanin Disambar 2015 zuwa Afirilun 2016.
Sun hada maki biyar da cin kwallo hudu da kai hari 26 a 2023, shine kwazo mara kyau a kakar nan.
Ta buga karawa hudu ba tare da cin kwallo ba, wadda ba ta zura kwallo ba a minti na 45 da fara wasa daga 11 da ta fafata a 2023.
Sun yi kan-kan-kan da tarihin doke su wasa 12 a Premier League a bara.
Crystal Palace ta yi rashin nasara a wasa 17 a Premier League a bana a karawa da kungiyoyin goman farko a teburi da canjaras takwas aka doke ta tara.
Wasa 10 Wilfried Zaha ya yi amma bai ci kwallo a bayan nan a Premier League appearances.