
Asalin hoton, OTHER
A gasar Premier League ta Ingila Arsenal ta cigaba da zama daram a teburi, bayan kurman duro da ta yi da Newcastle.
An buga wasan ne a filin Gunners na Emirates, kuma a karon farko a kakar bana Arsenal ta gaza cin wasa a gida.
A sauran wasanni Manchester United ta cigaba da zama na hudu, bayan doke Bournemouth a Old Trafford 3-0.
Luke Shaw da Casemiro da kuma Rashford ne suka ci kwallayen.
Sai kuma Leicester da tayi rashin nasara har King Power a hannun Fulham, daya mai ban haushi.
To amma Everton ce ta fi jin jiki, bayan da Brighton ta sharara mata hudu a Goodison Park.
An tashi wasan 4-1, kuma itace rashin nasara ta uku da Everton ta yi jere a gidanta.
Hakan ya kara saka matsin lamba ga kocin kungiyar Frank Lampard, wanda ya ci wasa daya a cikin tara a bana.