
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta amince kulla yarjejeniya da dan wasan Ukraine Mykhaylo Mudryk mai shekara 21 a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da kulob dinsa Shakhtar Donestsk kan kudin da za a biya. (Nicolo Schira)
Real Madrid da Chelsea da Manchester City sun mayar da dan wasan bayan RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol mai shekara 20 mutum na farko da suke nema. (Sport-in Spanish)
Tottenham da Liverpool na daga cikin kulob din Firemiya da a shirye suke su sayi dan wasan Slovakia Milan Skriniar mai shekara 27 wanda kwantiraginsa a Inter Milan zai kawo karshe a karshen wannan kaka. (Teamtalk)
Arsenal na daf da amincewa da sabuwar yarjejeniya da dan wasan Brazil mai shekara 21 Gabriel Martinelli. (Fabrizio Romano)
Kulob din Saudiyya Al Nassr na da burin sayan dan wasan Faransa mai shekara 31 N’golo Kante idan kwantiraginsa ya kare a Chelsea a karshen kaka. (Footmercato – in French)
Tottenham na sa ido kan Manuel Ugarte a Sporting Lisbon inda dan wasan mai shekara 21 na Uruguay ke gwagwarmayar saka hannu a sabon kwantiragi da kulob din na Portugal. (Record – subscription required)
Newscastle da Juventus da Borussia Dortmund na daga cikin kungiyoyin da ke son sayen dan wasan bayan Real Valladolid da Sifaniya mai shekara 18 Ivan Fresneda. (Fabrizio Romano)
Wolverhampton na son samun sabon gola domin yi wa golan Portugal Jose Sa mai shekara 29 kishiya. (Express and Star)
Aston Villa ta soma tattaunawa da Villarreal domin kulla yarjejeniya kan dan wasan Netherlands Arnaut Danjuma mai shekara 25. (Todofichajes – in Spanish)
Inter Milan na tunanin sayen dan wasan bayan Roma da Inga mai shekara 33 Chris Smalling. (Calciomercato – in Italian)
Newscastle ta soma tattaunawa dan dan wasan Flamengo mai shekara 18 dan kasar Brazil Matheus Franca. (Globo – in Portuguese)