Arsenal za ta sayar da ‘yan wasa domin cefanen gasar Zakarun Turai, Walker ba ya son barin Man City'Yan wasan Arsenal

Asalin hoton, OTHERS

Dan bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker, yana son ya ci gaba da zama a kungiyar duk da rashin sanya shi a wasa sosai a wannan kakar da kuma sha’awar ɗaukarsa da Aston Villa da AC Milan ke yi. (Star)

Newcastle da Manchester City sun fice daga jerin masu neman dan wasan tsakiya na Chelsea Mason Mount, kuma ana sa ran dan Ingilan zai bar Stamford Bridge a bazara. (Football Insider)

Amma ita kuwa Arsenal har yanzu tana son Mount wanda hakan ke nufin za ta hakura da zawarcin Declan Rice na West Ham da Ingila. (Mail)

Bayern Munich kuwa na sha’awar dan gaban Aston Villa Ollie Watkins, dan Ingila a madadin Harry Kane, idan ba su samu kyaftin din na Ingila ba. (Mirror)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like