
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana dalilin da ya sanya shi saka David Raya a wasan Premier League da Everton, maimakon babban golan ƙungiyar, Aaron Ramsdale ranar Lahadi.
Raya, wanda ya koma wasannin aro daga Brentford bana, ya fara buga wa Arsenal karawar Premier League da ta yi nasarar cin 1-0.
Ramsdale ya yi wasa 38 a Gunners a kakar da ta wuce.
“Ya ce tsari ne kamar yadda Fabio [Vieira] ko Eddie [Nketiah] ke buga wasanni maimako Gabriel Jesus,” in ji Arteta.
“Ban taɓa jin ana tambayar dalilin da ya sa Gabriel Jesus ba ya buga wasanni ba, wanda ya lashe kofuna fiye da kowa har da ni kaina.
”Ba yadda zan yi na saka ‘yan wasa biyu masu buga gurbi ɗaya a lokaci ɗaya. David yana da ƙwarewa da gogewa kamar Aaron, kuma hakan ci gaba ne a ƙungiyarmu.
Arsenal za ta buga Champions League a karon farko tun kakar shekara ta 2016/17, inda za ta karɓi baƙuncin PSV Eindhoven ranar Laraba kafin ta karɓi baƙuncin Tottenham ranar Lahadi a wasan hamayya.
Arteta ya ce zai ci gaba da sanya Ramsdale da Raya a wasannin kakar bana.