Ashe Yusuf Buhari Ba Shi Kadai Yayi Hadarin Ba



Sabbin rahotanni sun nuna cewa, a lokacin da dan Shugaban Kasa, Yusuf Buhari ya yi hadari da Babur din yana tare da babban abokinsa, Bashir Gwandu wanda shi ma, a halin yanzu yana kwance a asibitin Cedarcrest da ke Abuja cikin mummunan yanayi.

Jaridar ‘ Daily Nigerian’ ta ruwaito wata majiya wadda ta yi karin haske kan hadarin inda majiyar ta nuna cewa hadarin ya auku ne a lokacin da abokan biyu ke tseren Babur din a yankin Gwarimpa.

Majiyar ta nuna cewa Yusuf ne ke kokarin wuce abokin nasa, sai Babur din ta kwace masa wanda na take ya bugi Babur din abokinsa kuma nan take suka wuntsula. Majiyar ta ce, jami’an tsaron da ke kula da tsaron Lafiyar Yusuf Buhari sun nemi Izinin kai yaran biyu asibiti sai dai a yanzu, duk hankali ya dauke kan dan Buhari, babu wanda ya damu da halin da Bashir Gwandu ke ciki.

You may also like