Asiri Ba Ya Tsorata ni – Gwamna Badaru


 

Jigawa-State-2

Gwamnan jahar Jigawa Badaru Abubakar ya bayyana cewa baya tsoron asirin mutanen jahar Ondo kuma zai gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jahar da gaskiya da rikon amana.

Gwamnan ya fadi haka ne  yayin da yake magana da manema labarai a Abuja bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin zaben fidda gwani a jahar ta Ondo na jam’iyyar APC.

 

Ya ce yin zabe da gaskiya da rikon amana shi zai warware barakar da ke da akwai tsakanin ‘yan jam’iyyar na jahar. “Idan suka yarda cewa munyi zabe da gaskiya, tabbas za su yarda da sakamakon”.

Da aka tambayeshi ko ba ya jin tsoron agumin mutanen na Ondo, ya bayyana cewa shi ko yarda da asiri bai yi ba ballantana ya ji tsoro.

Izuwa yanzu dai barakar jam’iyyar APC a jahar Ogun ta sanya an daga zaben fidda gwanin har sau biyu. Akwai yiwuwar zaben zai gudana a gobe 1 ga watan Satumba.

You may also like