Assad ya gabatar da shirin afuwa ga ‘yan tawayen Syria


Shugaban Syria Bashar al Assad ya gabatar da shirin afuwa ga ‘yan tawayen kasar da ke gwabza yaki da dakarunsa, matukar sun amince su mika wuya.

Shugaba Assad ya bayyana cewa, duk dan tawayen da ya ajiye makaminsa, to zai kubuta daga duk wani nau’i na azabtarwa da kuma fushin shari’a kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SANA ya rawaito kamalan shugaban.

Kazalika, duk dan tawayen da ya saki mutanen da aka yi garkuwa da su zai ci gaciyar wannan shirin na afuwa kamar yadda SANA ya ce.

Shirin na afuwar na zuwa ne, a yayin da dakarun da ke goyon bayan gwamnati suka yi wa ‘yan adawa a birnin Aleppo kawanya, inda ake fargaban mutane fiye da dubu 200 sun shiga tarko.

A cikin wannan makon nan ne, jakadan majalisar dinkin duniya a Syria, Staffan de Mistura ya bayyana fatan ganin an koma teburin tattaunawar zaman lafiya nan da karshen watan Agusta mai zuwa don kawo karshen zubar da jini da aka kwashe fiye da shekaru biyar ana yi.

Sama da mutane dubu 280 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da yakin Syria ya barke a shakara ta 2011.

You may also like