
Asalin hoton, Reuters
Aston Villa na son sayar da ɗan wasan tsakiyar Brazil Philippe Coutinho a watan Janairu, shekara guda kenan bayan ɗan wasan mai shekara 30 ya isa Villa Park. (Football Insider)
Kocin Villa Unai Emery ba ya so ya yi aiki da golan Argentina Emiliano Martinez mai shekara 30 kuma yana so ya sayar da golan wanda ya ci gasar kofin duniya a wata mai zuwa. (Fichajes – in Spanish)
Akwai yiwuwar Liverpool ta haƙura da sayen ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham saboda suna ganin ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan mai shekara 19 lamari ne mai sarƙaƙiya. (AS – in Spanish)
Atletico Madrid ta ƙulla yarjejeniya da Caglar Soyuncu har zuwa 2027 haka kuma ɗan wasan mai shekara 26 na Leicester da Turkiyya ana sa ran zai shiga kulob ɗin a watan Janairu duk da cewa zai iya tafiya a kyauta ne kawai a watan Yuli. (Nicolo Schira)
Chelsea ce kan gaba a masu son sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila Declan Rice a daidai lokacin da ɗan wasan mai shekara 23 ya shiga watanni 18 na ƙarshe a zamansa a West Ham. (Athletic – subscription required)
Dole ne Chelsea ta mayar da ɗan wasan bayan RB Leipzig Josko Gvardiol mai shekara 20 ɗan wasa mafi tsada a tarihi idan tana so ta sayi ɗan wasan na Croatia a watan Janairu. (Football London)
Liverpool da Tottenham na daga cikin manyan kulob din gasar Firemiya da suke son sayen ɗan wasan bayan Inter Milan da Slovakia Milan Skriniar mai shekara 27. (Teamtalk)
Ɗan wasan gaban Uruguay Luis Suarez mai shekara 35 ya shirya tsaf domin komawa kulob ɗin Brazil Gremio kan kwantiragin shekara biyu. (Cesar Luis Merlo, via Mail)
Rahotanni na cewa Atletico Madrid na shirin barin ɗan wasan Portugal Joao Felix mai shekara 23 ya tafi aro zuwa kulob ɗin da ke gasar Firemiya muddin kuɗaɗe da ɗawainiyarsa ɗayan kulob ɗin zai ɗauka. (Mirror)
Ɗan wasan tsakiyar Angers da Morocco Azzedine Ounahi mai shekara 22 ya ce har yanzu bai yanke hukunci ba kan makomarsa duk da Leicester da Leeds United da West Ham na nemansa. (Goal)
Tottenham na sunsuna ɗan wasan Sifaniya Bryan Gil mai shekara 21 da ɗan wasan Senegal Pape Sarr mai shekara 20. (Relevo, via Mail)