
Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa na muradin dauko dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 27, daga Manchester City. (Football Insider)
Dan wasan gefe na Ingila Ben Chilwell, mai shekaru 26, ya shirya tsaf domin rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu a kungiyar Chelsea. (Athletic – subscription required)
Mahaifin Lionel Messi da eja din shi Jorge, sun gana da Barcelona amma babu batun wani tayi da aka yi kan dan wasan gaba na Argentina may shekara 35. (Cadena Ser, via Mirror)
Dan wasan tsakiyar Jamus Marco Reus, mai shekara 33, ya shirya domin kammala yarjejeniya da Borussia Dortmund to amma zai zaftare albashinsa matuƙar yana muradin ci gaba da zama a ƙungiyar. (Bild – in German)
West Ham kuwa na sanya ido kan mai tsaron bayan Manchester United, Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 25, a kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)
Arsenal da Chelsea na daga cikin ƙungiyoyin da suke nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan baya na Jamus, mai shekara 25. (Bild – in German)
Chelsea na fatan cigaba da zaman Joao Felix zuwa kakar wasa mai zuwa. A watan Junairu da ya wuce ne, Chelsea a rattaba hannu kan kwantiragin dan wasan tsakiyar na Portugal mai shekara 23 daga Atletico Madrid a matsayin aro a watan Junairu.. (Fabrizio Romano)
Newcastle United na son dauko dan wasan gaba na Brazil Joao Pedro, mai shekara 21,daga Watford a lokacin bazara. (Football Insider)
Brighton na da yakinin sabun kwantiragi da matashin dan wasan gaba na jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, duk da zawarcinsa da kungiyoyin Manchester United da Tottenham ke yi. (Mail)
Har wa yau, Brighton na fatan dauko dan wasan tsakiya na Ingila Reiss Nelson mai shekara 23 a kakar wasa da mu ke ciki. (Mail)
Liverpool kuma dan wasan tsakiya ajin kasa da shekaru 19 na Bristol City Alex Scott a wannan kakar, to amma West Ham da Wolves na cikin masu zawarcin dan wasan mai shekara 19. (Mail)