ASUP: Duk wanda ya shiga yajin aiki zai ji a aljihun sa-FG


Chris-Ngige-2

 

Kungiyar ASUP ta Malaman Makarantun koyar da aiki na Polythechnic sun tafi yajin aiki na mako daya kuma sun ce babu maganar ja da baya a kan batun na su. To sai dai fa Gwamnati ta dauki wani mataki mai tsanani ga masu yajin.

Gwamnatin tarayya tace za ta dabbaga tsarin nan na babu aiki-babu albashi ga masu yajin aikin. Wani Jami’in Gwamnatin tarayya ya bayyana haka a Abuja. Malaman Makarantun na gaba da Sakandare sun tafi yajin aikin ne a tsakar daren shekaran jiya.

Ministan kwadago na Kasa Chris Ngige yayi yunkurin a sasanta da Gwamnati, sai dai abin duk ya ci tura. Kungiyar tace kaf ma’aikatan na ta za su tafi yajin aikin na mako guda na gargadi, shi kuwa Ministan yace bai san wani Yajin gargadi ba a dokar aiki.

Da alamu dai Ministan zai yi amfani da tsarin ‘Ba aiki-ba kudi’ ga Ma’aikatan da suka tafi yajin. Yanzu haka dai Ma’aikatar Ilmi na cigaba da tattaunawa da ‘Yan Kungiyar ASUP din. Ministan dai yayi kira da Kungiyoyin da su tsaya ayi sulhu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like