Asusun lamuni na duniya IMF yace tattalin arzikin Najeriya zai habaka fiye da na kasar Afirika ta Kudu.
Wannan dai wani koma bayane kan hasashen da tun farko asusun yayi a watan Yuli inda yace tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu zai habaka da kaso 1% yayin da na Najeriya zai habaka da kaso 0.88%.
Da yake magana ranar Talata lokacin da ake bayyana rahoton yadda tattalin arzikin duniya zai kasance, a hedikwatar hukumar dake birnin Washington, babban jami’in dake kula da fannin tattalin arziki a asusun, Maurice Obstfeld, yace rikicin siyasa da kuma rashin kwarin gwiwar da yan kasuwa da kuma masu siyayya suke dashi a kasar Afirka ta Kudu.
Yayin da ake sa ran habakar tattalin arzikin Najeriya zai cigaba da bunkasa da kaso 0.88 cikin dari, shi kuwa na kasar Afirka ta kudu zai yi kasa zuwa kaso 0.77 cikin dari.
Asusun ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin duniya zai bunkasa da kaso 3.8% cikin dari nan da shekara ta 2021.