ASUU Ta Caccaki Ngige Kan Rijistar Sabbin Kungiyoyi Da Za Su Maye Gurbinta
Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da aka kasa cimma matsayar kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi da a yanzu ya kai tsawon wata takwas.

A ranar Talata ne ministan kwadago da ayyuka a Najeriya Dakta Chris Ngige ya mika takardar shaidar rijistar wasu kungiyoyi biyu da suka hada da kungiyar likitoci da fannin samar da ilimin hakora wato NAMDA da kuma Gamayyar kungiyar malaman jami’a ta kasa wato CONUA, wadanda a cewarsa za su yi aiki kafada da kafada da takwararsu ASUU.

Sai dai wannan yunkuri ya gamu da kace-nace inda ‘yan kasar ke ganin an yi hakan ne don karya lagon kungiyar ASUU, batun da mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU Mr. Chris Pimuwa ya ce barazana ce kawai wadda ba zata kai gwamnati ko’ina ba.

Batun yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ya sauya salo sosai, la’akari da cewa har yanzu an kasa cimma matsaya tsakanin kungiyar da gwamnati, lamarin da wasu ke ganin laifin gwanati wajen kasa cika bukatun kungiyar da kuma tausayawa dalibai, a cewar Dakta Muhammad Nuwaila malamin kwalejin ilimi a Najeriya.

Shi ma malam Abdurazak Adamu ya ce wannan yunkuri da gwamnatin kasar ta yi ba zai haifar da da mai ido ba.

Ko a wannan makon sai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi kungiyar ASUU da hannu a ayyukan cin hanci da rashawa a bangaren ilimi na kasar.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 ne dai malaman jami’o’in suka fara yajin aiki saboda rashin cika alkawuran da gwamnati ta dauka na biyansu wasu kudade na alawus-alawus da kuma bukatar inganta rayuwarsu.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

You may also like