Atiku Da Tinubu Sun Fara Kokarin Fita Daga Jam’iyyar APC


Rikicin Jam’iyyar APC na daukar sabon salo. Hujjoji sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fara kulla wata alaka tsakanin sa da jagoran Jam’iyyar na kasa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, domin neman mafita a babban zaben 2019. Sai dai ana fargabar wannan alaka za ta iya wargaza Jam’iyyar APC sakamakon fara tunanin kirkirar sabuwar Jam’iyya da suke yi. Kamar yadda majiyar jaridar Daily Trust ta ruwaito. 
Jaridar ta jiyo daga kwakkwarar majiya ta Jam’iyyar APC cewa, “Tinubu An alliance na kwakkwaran shiri tsakanin sa da Atiku na ficewa daga Jam’iyyar tare da Gungun Masoyansu matukar Buhari ya ci gaba da tafiyar da shugabanci a yadda ya ke yi yanzu”.

You may also like