Atiku na  ganawa da shugabannin jam’iyar PDP


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na ci-gaba da ganawa da shugabannin jam’iyar PDP a cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

Abubakar ya fice ne  daga jam’iyar APC ranar juma’ar da ta gabata.

A sanarwar da ya fitar ta barin jam’iyar, Abubakar ya soki shuwagabannin APC  inda yace jam’iyar ta dauko hanyar mutuwa.

Ya zuwa yanzu tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gana da shugabannin jam’iyar PDP na jihar Adamawa dake kowanne mataki da kuma shugabannin jam’iyar na jihohi 6 dake yankin arewa maso gabas.

An kuma ce ya gana da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP mai kula da yankin arewa maso gabas.

Abdullahi Prambe, sakataren jam’iyar PDP na jihar Adamawa ya ce ganawar tasu ta haifar da, ɗa mai ido.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like