Atiku Ya Fi Kowa Cancanta Da Shugabancin Najeriya – Farfesa Dupe OlatuboWani masanin tattalin arzikin Noma Farfesa Dupe Olatubosun ya bayyana cewa, Tsohon Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Atiku Abubakar kuma daya daga cikin jigon Jam’iyyar APC ya cancanci shugabancin Nijeriya.

Olatubosun dake malamin Jami’a kuma mai rike da  masana’antu daban daban ya yi la’akari da irin halin matsin da kasa ke ciki a yanzu tare da cewa shuwagabanni irin su ne zasu iya saita kasa kuma shi ya cancanci shugabancin Nijeriya

Ya ce kwarin guiwarsa na sanin yadda ya kamata a tafiyarda harkokin kasa musamman a lokacin da Nijeriya ke fama da matsaloli barkatai yasa ya bayyana haka.

Farfesan yace taimako da Atiku ke yi da himmarsa na cigaban inganta bangaren Ilimi yasa ya fita daban daga cikin wasu shuwagabannin,kuma yana daya daga cikin mutanen da kasa ke bukata a yanzu don saita yanayin yadda harkoki ke tafiya kuma shi zai iya raya cigaba tattalin arzikinta a matsayinsa na wanda ya taba mulkan Nijeriya.

You may also like