Atiku Ya Isa Kano Don Karbar Shekarau Da Ke Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da sauran shugabannin jam’iyyar sun sauka a Kano.

Babbar jam’iyyar adawar na shirin karbar tsohon gwamnan jihar, wacce ke arewa maso yammacin Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ke shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP.

A makon jiya ne dai Sanata Shekarau ya bayyana fitar sa daga Jam’iyyar ta NNPP biyo bayan tsamin dangantaka tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ke yi wa NNPP takarar shugaban kasa.

“Gabanin gangamin da jam’iyyar PDP za ta yi a Kano…..don karbar mai girma Ibrahimn Shekarau da sauran wadanda za su sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa babbar jam’iyyarmu.

“Shugaban jam’iyya na kasa, Sen. Dr Iyorchia Ayu, da shugaba mai shirin karbar mulki, Atiku Abubakar da sauran shugabannin jam’iyya sun isa jihar don halartar wannan taro da aka dade ana jira.” Jam’iyyar PDP ta fada cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook dauke da bidiyon isar Atiku jihar.

A watan Mayun bana ne dai Sanata Shekarau ya shiga Jam’iyyar NNPP bayan ficewar sa daga Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, al’amarin da ya sanya wasu ke sukan matakin tsohon Gwamna.

“Da ma mu akidarmu, duk inda za a yi zalunci, babu adalci, babu mu a wurin. Da a ce kawai wata bukatata ce ko bukatar wasu daga cikin wadanda muke shugabanci tare da su, ai da wannan gayyar ta al’umar Kano, da ba su mana biyayya ba.” Shekarau ya ce yayin hirarsu da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

A ranar Litinin din nan ake sa ran za a karbi Shekaru da magoya bayansa hade da wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a jam’iyyar ta PDP.

Saurari cikakkiyar hirar anan:

You may also like