Atiku ya musalta cewa ya kai wa Jonah Jang ziyara a gidan yari


Toshon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya musalta cewa ya kai ziyarar goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Plataeu, Jonah Jang, wanda ke tsare a gidan yari kan zargin da ake masa na barnatar da kudaden jihar lokacin da yake kan mulki.

Luka Ayedoo, jami’in hulda da jama’a na hukumar dake lura da gidajen yari ta kasa a jihar Plataeu shine ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa Abubakar tare da wasu jiga-igan jam’iyar PDP sun ziyarci tsohon gwamnan.

“A karshe mako mun karbi bakuncin, Farfesa Jerry Gana, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma wasu fitattun yan Najeriya da suka kai ziyarar goyon baya ga Sanata Jonah Jang,” ya fadi haka.

Amma a sanarwar da ya fitar Atiku ya musalta ziyarar inda ya bayyana wuraren da ya ziyarta a cikin kwanaki uku da suka gabata.

A karshe sanarwar ta ce har yanzu mataimakin shugaban kasar yana Yoka babban birnin jihar Adamawa.

You may also like