Atiku Ya Musanta Ziyartar Jang A Gidan Yari


Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya musanta rahoton da ake yayatawa kan ya ziyarci Tsohon Gwamnan Filato, Sanata Jonah Jang wanda ake tsare da shi a gidan kurkuku bisa tuhumar cin hanci da rashawa.

Ana dai ci gaba da yayata rahotannin cewa wasu ‘yan siyasa sun ziyarci tsohon Gwamnan gidan kurkukun da ake tsare da shi. Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzkin kasa ta’anati (EFCC) ce ta gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhumar almundahana da kudi fiye da naira biliyan shida lokacin da
yake rike da mukamin gwamna. A ranar 24 ga watan Mayu ne za a ci gaba da sauraren karar.

You may also like