Atiku ya ziyarci FayoseTsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gana da Ayo Fayose gwamnan jihar Ekiti kuma jagoran jam’iyar PDP a jihar.

Jirgin saman Atiku ya sauka a filin jirgin saman Akure safiyar ranar Litinin kafin daganan ya wuce zuwa Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti.

Fayose ya jagoranci shugabannin PDP zuwa Akure inda suka tarbi tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Atiku wanda yace yazo Ekiti ne saboda matsayin Fayose na jagoran yan adawa kuma shugaban gwamnonin jam’iyar PDP.

Ya ce ba yaje Ekiti bane domin yaƙin neman zaɓe  bane face zuwa domin tattaunawa kan inda za su sa gaba.

“Tun bayan dawowata cikin jam’iyar PDP wannan ce jiha ta farko da na fara ziyarta domin tattaunawa da shugabanni da kuma ƴaƴan jam’iyar,” ya ce.

“Ni da Fayose mun ƙulla abota tun lokacin da yake gwamna a zangon mulkinsa na farko kuma ina girmama shi akan haka.”

Sai dai Atiku yaƙi cewa komai kan wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubutawa Buhari inda ya nemi kada ya sake tsayawa takara a shekarar 2019.

You may also like