Atiku Ya Ziyarci ShekarauBabu shakka alamu na nuni da cewar ana daf da fara kada gangar siyasa domin shiga zabukan shekarar kai da halinka. A ranar Asabar 18/11/2017 tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan kano Sardaunan Kano kuma dan takarar shugabancin Najeriya a shekarar kai da halinka wato 2019 a gidansa dake unguwar Mundubawa Inda aka gabatar da wani dan kwarya-kwaryar taro a dakin taro na HAFSAT HALL dake gidan na Sardauna.

Ko shakka babu wannan ziyara nada nasaba da goyon bayan shi kansa Atiku ga takarar Malam Shekarau duk kuwa da cewar akwai bambanci gare su a jam’iyyance.

You may also like