Attajirai Biyar ‘Yan Najeriya Da Zasu Iya Ciyar Da Mutanem Kasar nanOxfam International ta fitar da wani kwakkwaran binciken da ya bayyana cewa hamsahakan ‘yan Nijeriya biyar za su iya ciyar da kasar nan baki dayanta. Rahoton ya ce su biyar din idan aka hada dukiyar su wuri daya, za ta kai adadim Dalar Amurka Bilyan 29.9.
Rahoton wanda suka bayyana da suna ‘Rata tsakanin Attajirai Da Talakawa A Nijeriya’, ya bayyana mummunar rata da bambanci a tsakanin attajirai da fakirai a kasar nan. An fallasa cewa wasu attajirai ne ‘yan kalilan ke tatse amfanin tattalin arzikin kasar nan.
Har ila yau, wannan rahoton ya ce wannan matsanancin rata tsakanin attajirai da matalauta, ta na daya daga cikin sabubban rincabewar rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabacin Nijeriya.
Rahoton ya kuma nuna cewa abin da babban attajirin Najeriya (Aliko Dangote) ke samu a rana daya, ya nunka abin da talaka ke kashewa a bukatun sa na dole na shekara daya har sau dubu takwas.
An kuma kara da cewa sama da mutane miliyan 112 ne ke rayuwa a cikin katutun talauci a kasar nan, amma duk da haka, kafin babban attajirin Nijeriya ka karad da kudin sa, sai ya yi shekara arba’in da biyu, 42 ya na kashe Dala Miliyan 1 a kullm daga cikin kudin sa.
Ci gaban rahoton binciken ya kara tabbatar da cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashe kalilan wadanda al’ummar ta ke fama da talauci, duk kuwa da habbaka da tattalin arzkinta ke ci gaba da yi.
Wani karin abin damuwa a rahoton shi ne yadda ya bayyana cewa kashi 69 na al’ummar Arewa maso Gabacin Nijeriya, su na rayuwar fakiranci ne, ba talauci ba. Yayin da fakirai a Kudu maso Yammacin Nijeriya ba su wuce kashi 49 ba.
Baya ga wannan, an nuna cewa akasari mata ba su ma san ana samun ci gaban tattalin arziki ba, saboda mafi yawa an bar su a baya ne wajen gudanar da kananan aiyuka ko sana’o’in da ba su iya biya wa mace bukatun yau da kullum na rayuwa.
An kuma ce daga cikin al’ummar da ke zaune a karkara, mata sun kunshi kashi 60 zuwa 79, kuma kafin ka samu mace daya mai gonar kan ta, ka samu namiji biyar da gonaki.
Rahoton ya ci gaba da cewa mata ba su samun damar samun ilmin zamani kamar mazaje. Kashi 3 bisa 4 na matalauta da fakiran da rahoton ya bayyana, ya ce duk mata ne ba maza ba.
“Har yau talaka bai amfana daga dimbin arziki da Allah ya yi wa Nijeriya ba, saboda illar wawurar kudade da masu mulki da manyan ma’aikata ke yi. da kuma kaka-gidan da manyan ‘uyan kasuwa da attajirai su ka yi a jikin gwamnati da sauran masu fada a ji a sha’anin mulki.
Rahoton ya ce manyan masu rike da mukamai da manyan ma’aikatan gwamnati sun sace kimanin Dalar Amurka Tiriliyan 20 tsakanin 1960 zuwa 2005, yayin da kamfanonin kasashen waje sun yagi na su rabon kimanin Dala Bilyan 2.9 a kowace shekara.
Abin takaici kamar yadda rahoton ya nuna, yayin da a gefe daya ake kassara Nijeriya ta hanyar satar kudade, su kuma kananan masana’antu da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kan su,ba a tsinana musu komai sai ma harajin da ake yawan damfara musu daban-daban.
Duk da cewa Nijeriya ce kasar da ta fi sauran kasashen Afrika karfin tattali, kasafin kudin da ake warewa ga fannin ilmi, kiwon lafiya da sauran fannonin da al’umma za su ci moriyar rayuwa, kalilan ne idan aka kwatanta shi da kasafin sauran kasashen da ke yankin.
Idan za a iya tunawa, cikin 2012, Nijeriya ta kashe kashi 6.5 kacal na kasafin kudin ta a fannin ilmi, yayin da ta kashe kashi 3.5 kacal a fannin inganta kiwon lafiya. Yayin da Ghana ta kashe kashi 18.5 bisa 100 a fannin ilmi, a fannin kiwon lafiya kuma ta kashe kashi 12.8 na kasafin ta na 20015.
“A yanzu kimanin ‘yan Nijeriya milyan 57 ba su samun tsaftaccen ruwan famfo, milyan 130 kuma ba su da kyakkyawan muhalli mai tsafta, ga kuma yara kanana sama da miliyan 10 da ke gararamba saboda an ki sanya su makarantu.” Haka rahoton ya bayyana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
Uku daga cikin hamsahakan attajiran Nijeriya biyar, sun hada da Aliko Dangote, Femi Otedola da kuma Fulorunsho Alakija, wadda ita mace ce.
Marigayi Sani Dan Indo mai waka, tuni ya bayyana wannan bambanci ko ratar da ke tsakanin attajirai da matalauta a cikin baiti daya na wata wakar sa:
“Wallahi duniyar Allah haka nan ta ke,
In wani ya tara ya aje,
Na ga ga wani ba shi da sisi.”
Shi kuwa Marigayi Danmaraya Jos, a cikin wakar da yi wa lebura, wadda Marigayi Muhammadu Maiturare ya rubuta, Danmaraya ya rera, ya ce:
“Fatara mai sa a sangarce,
Ta hana wa mutum ya san rance,
Yunwa mai kai maza kwance,
Ta kashe ba sai da aibi ba.”
To ko akwai alamomin yin duba ko nazarin wadannan baitoci domin a ceto talaka daga kunci, fatara da talaucin da ya ke ciki? A gane mana hanya.

You may also like