Attajirai Takwas Ne Suka Mallaki Duniyar Nan –  Oxfam Attajirai takwas da suka fi kudi a duniya sun mallaki kwatankwacin dukiyar mutum biliyan 3.6 wadanda su ne rabin mutanen duniya da suka fi talauci, inji kungiyar agajin Oxfam
Kungiyar agajin ta ce, alkallumanta, wadanda masu suka suka musantawa, sun zo ne daga ingantattun asali kuma gibin dake tsakanin masu kudi da marasa galihu ya fi yadda ake zato girma.
Rahoton Oxfam ya zo ne daidai lokacin da ake fara taron tattalin arzikin duniya a Davos. Wasu sun soki rahoton , suna masu cewa za’a iya kawar da talauci ne ta habaka tattalin arziki.
Attajiran da suka fi kudi a duniya
1. Bill Gates (Amurka): daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin Microsoft (yana da akalla dala biliyan $75)
2. Amancio Ortega (Spaniya): wanda ya kafa Zara mai Inditex (yana da akalla dala biliyan $67)
3. Warren Buffett (Amurka): wanda ya mallaki akasarin hannayen jari a Berkshire Hathaway (yana da akalla dala biliyan 60.8)
4. Carlos Slim Helu (Mexico): mai Grupo Carso (yana da akalla dala biliyan 50)
5. Jeff Bezos (Amurka): wanda ya kafa kuma shugaban Amazon (yana da akalla dala biliyan 45.2)
6. Mark Zuckerberg (Amurka): daya daga cikin wadanda suka kafa kuma shugaban Facebook (yana da akalla dala biliyan 44.6)
7. Larry Ellison (Amurka): Daya daga cikin wadanda suka kafa kuma shugaban Oracle (yana da akalla dala biliyan 43.6)
8. Michael Bloomberg (Amurka): Mai Bloomberg LP (yana da akalla dala biliyan 40)

Daga : Jerin sanayen attajira na mujallar Forbes , na watan Maris din shekarar 2016

You may also like