AU ta bude taro a Kigali


 

wannan lahadi shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Afirka ke bude taro a birnin Kigali dake Rwanda, daga cikin muhimman batutuwan da taron zai mayar da hankali akwai dangantakar kasashen da Kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague.

Shugabannin kasashen Afirka na cigaba da zargin kotun da yi wa shugabannin nahiyar bi-ta-da-kulli, inda suka fi son a kafa wata kotu ta musamman a nahiyar wadda za ta dinga hukunta tauyen hakkin bil’adama.

Taron na kwana biyu zai kuma tattauna a kan rikicin Sudan ta kudu, da kuma shirin kungiyar Tarayyar Afirka na yin Fasfo na bai-daya.

A wani labarin kuma, Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce Salva Kiir da Riek Machar sun ci amanar al’ummarsu.

Ban da a halin yanzu ke Kigalin kasar Rwanda, domin halartar taron AU karo na 27, ya bukaci Salva Kiir, da mataimakinsa Rick Machar dasu yi aiki domin al’umma.

Amma su sani, sun ci amanar ‘yan kasar su, sun kuma ci amanar kasashen duniya, da a ko wane lokaci ke fadi tashin ganin sun tallafawa kasar, amma kuma sun watsa masu kasa a ido, a cewar Mista Ban.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like