Auren Zawarawa A Jihar Kano: Amarya Ta Haihu A Daren Farko



Auren Zawarawa 1,520 daga kananan hukumomin jihar Kano ya bar baya da kura yayin da daya daga cikin Amaren Habiba Inusa ta haifi da Namiji a daren farko da Ango ya shiga domin raya sunnah. A cewar Habiba cikin na Angon nata ne Babangida. Duk da dai bai yi wata-wata ba ya gaggauta fatattakar ta daga gidan sa. Sai dai daga baya wanda  ake zargi da yi mata cikin ya cika wandonsa da iska. 

<!–Ads1–>
A yayin tuntubar kwamandan rundunar Hisbah na jihar Kano Malam Aminu Daurawa akan ikirarin da ya yi na cewa kowacce daga cikin Amaren an tantance lafiyar ta. Sai ya ce daga baya gwamnatin jihar Kano ta kwace abin daga wajen su ta damka shi ga ‘yan siyasa.

You may also like