
Asalin hoton, OTHER
Zambia ta nada tsohon kocin Chelsea Avram Grant a matsayin wanda zai horar da tawagar kasar ta Chipolopolo.
Dan kasar Israilar ya aminta da zama kocin na Zambia tsawon shekara biyu, kamar da yadda hukumar kwallon kafar kasar ta sanar.
”Ina son in fuskanci sabon kalubale, don haka na zabi Zambia,” in ji Grant a hira da manema labarai a Lusaka.
Grant ya kara da cewa burinsa shi ne ya gina wani abu da Zambia za ta yi alfahari da shi a nan gaba.
Avram Grant na da kwarewa wurin horarwa a Afrika, don ya taba kai Ghana wasan karshe na gasar kofin nahiyar Afrika, inda Ivory Coast ta doke su a bugun fenareti.
To amma ya yi murabus ne bayan karewa na hudu a gasar ta AFCON shekaru biyu bayan haka.
A baya Grant ya taba horar da Chelsea da West Ham sai kuma Ghana a matakin kasashe.