Ayarin motocin gwamnan Yobe sun sha ruwan duwatsu a Dapchi 


Daya daga cikin motocin da aka lalata a ayarin gwamnan

Wadi fusatattun mutane dake Dapchi a ƙaramar hukumar Busari ta jihar Yobe sun kai hari kan gwamnan jihar Ibrahim Geidam a ranar Alhamis.

Mutanen ba wai kawai sun riƙa yiwa gwamnan ihu bane a’a sai da suka yiwa ayarin motocinsa  ruwan duwatsu  ds kuma sauran abubuwa masu hatsari.

Geidam ya ziyarci garin ne domin sanar da mutane cewa ba a samu nasarar ceto ƴan matan kwalejin ƴan mata ta Dapchi jihar waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da su.

Mutanen da suka sace ƴan matan sun isa makarantar a ranar Litinin inda suka kwashe ƴan matan da har yanzu ba a iya tantance yawansu ba.

A ranar Laraba gwamnan yace sojoji sun samu nasarar ceto wasu daga cikin ƴan matan.

Amma a ranar Alhamis gwamnan ya sanarwa da mutane gaskiyar abinda yake faruwa a ƙasa.

Gwamnan da zuwansa garin ya shiga taron tattaunawa da masu riƙe da masarautun gargajiya kafin ya fara yiwa dandazon mutanen da suka taru a bakin fadar Hakimin.

Yana tsaka da jawabinsa mutane suka nemi sanin gaskiyar abin da yake faruwa anan ne fa gwamnan ya sheda musu cewar ba a samu nasarar ceto ƴan matan ba ya zuwa lokacin da yake musu jawabi jin haka ke da wuya wuri ya ɓarke da hayaniya ya yin da wasu suka shiga yin allah wadai ga gwamnati da kuma kungiyar Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like