Ba a Fito Zaben Gwamna A Jihar Legas Kamar Na Shugaban Kasa BaLEGOS, NIGERIA – Tunda sanyin safiya ne dai masu zabe suka fara isa cibiyoyin zabe duk da cewa dai malaman zabe sun makara don haka ba ko ina ne aka fara zabe da wuri ba.

Gwamnan legas Babajide Sanwo Olu ya kada kuri’ar sa ne a mazabar titin Lateef Jakonde dake Ikoyi a Legas tare da mai dakin sa. Suma ‘yan takaran Labour Party da PDP sunyi zaben ne a mazabun su.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)

Dukkannin su sun yaba da yadda ake zaben cikin nasara.

Wasu masu zabe da muka tattauna dasu, irin su Malam Nura Sufiyanu ya ce zabe an yi shi cikin lafiya, sai dai mutane basu fito ba, kuma dama basa fitowa.

Itama wata mata Hajiya Halimatu Usman, kira tayi da a fito ayi zabe kuma a barwa Allah komai domin samun shugabanni na kwarai.

Ta bangaren jami’an tsaro kuma an saka su lunguna da sakuna na birnin, banda wayanda ke shawagi ta jiragen sama.

Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibril:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like