
Asalin hoton, Getty Images
Frank Lampard ya ce baya jin za a magance matsalar Chelsea a rana daya, bayan da ya fara da kafar dama a Wolverhampton.
Lampard wanda ya ja ragamar Chelsea a karon farko a matakin rikon kwarya, ya yi rashin nasara 1-0 a gidan Wolves a wasan mako na 30 a Premier ranar Asabar.
Wasan farko da ya shugabancin Chelsea tun bayan wata 27 da aka kore shi a Stamford Bridge, Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.
Chelsea ta kasa zura kwallo a raga a wasa uku a jere kenan, karo na 11 da aka doke ta a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
”Aiki ne babba a gaba, in ji Lampard, wanda Chelsea ke mataki na 11 a teburin Premier League.
”Mun kwan da sani ba ma yanayi mai kyau, ba wanda muke bukata bane, amma da akwai dalilin hakan.”
”Ban jin zan warware matsalar nan a kwana daya, dole sai mun kara kwazo a wasa da sa kaimi.”