
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya ce Qatar ta yi nasarar shirya gasar cin kofin duniya da tarihi ba zai taba mantawa da ita ba.
Ya ce duka kasashen da suka samu halartar gasar sun bar Qatar da ke Gabas ta Tsakiya da wani abun alkhairi da ba zasu taba mantawa ba.
To amma babban abunda yafi jan hankali a hirar da ya yi da manema labarai shi ne, batun sauya gasar kofin duniya daga kasashe 32 zuwa 48.
Kuma za a fara aiwatar da hakan ne a gasar ta gaba, ta hadaka tsakanin kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.
Ana tunanin samar da rukuni 16 mai kasashe uku-uku, ko kuma rukuni 12 mai kasashe hudu-hudu.
A karkashin sabon tsarin nahiyoyi za su samu karin kason kasashen da za su wakilce su, inda ake hasashen Afrika za ta samu gurabu tara.
Za kuma a fadada gasar kungiyoyin duniya 32, da zasu buga tsakaninsu a gasar da ya kira FIFA Club World Cup ta maza da ta mata.
A gasar France 98 ce FIFA ta fadada gasar kofin duniya zuwa 32.