
Asalin hoton, OTHER
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce duniya ba ta taba shaidar wani dan kwallo ba kamar kyaftin din Argentina Lionel Messi.
Messi ya jagoranci kasarsa lashe kofin duniya na farko tun bayan 1986, bayan da Argentina ta lashe kofin duniya na Qatar 2022.
Dama kofin duniya ne kawai ya rage wa Messi ya ci a manyan kofuna, don a bara ne ya ci kofin Copa America.
Dan wasan mai shekaru 35 ya ci kofunan La Liga 10, na Zakarun Turai hudu da kuma Copa Del Rey bakwai a zamansa Barcelona.
Kuma mafi yawan kofunan ya ci da kungiyar yana karkashin horarwar Pep Guardiola, wanda ya yi aiki a Barcelona daga 2008 zuwa 2012.
”Kowa na da ra’ayinsa, amma kuma ba bu wanda zai yi tababa cewa shi ne dan wasan da duniya bata taba ganin irinsa ba.” In ji Guardiola.
Ya kara da cewa ” na sha fada cewa a ganina ba bu kamar shi.”
”Masu ganin Pele da Di Stefano da Maradona a matsayin gwanayensu sun yi dai-dai. To amma yanzu da ya lashe kofin duniya labarin Messi ya sake canzawa.”
Messi ya kafa tarihin zama gwarzon gasar kofin duniya har sau biyu a 2014 da kuma 2022, kuma ya fi ko wane dan wasa buga wasanni a gasar da 26.
Kazalika ya kafa tarihin cin kwallaye a ko wane wasa tun daga na rukuni har zuwa wasan karshe.