Ba Bu Wani Bature Da Muka Kama A SAMBISA –  Burutai Shugaban Rundunar Sojan kasa ta Nijeriya, Janar Tukur Burutai ya karyata rahotannin da ake ta yayatawa kan cewa rundunar soja ta kama wani Baturen kasar Faransa a lokacin da rundunar ta fatattake mayakan Boko Haram daga hedkwatarsu da ke Sambisa.
Burutai ya ce, sojoji dai sun kashe wani dan Boko Haram mai jan launin fata amma ba Bature ba ne. Ya kara da cewa hoton Baturen da ake ta yayatawa na wani Baturen Jamus ne wanda sojojin Kamaru suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon lokaci.
Haka nan kuma, Burutai ya bayyana cewa a lokacin da sojoji suka kaddamar da farmaki kan hedkwatar mayakan Boko Haram, Shugabansu, Abubakar Shekau da shi da manyan makarabbansa sun arce zuwa wata boya wanda kuma a halin yanzu sojojin na ci gaba da farautarsa

You may also like