
Asalin hoton, OTHER
Tsohon kyaftin din Super Eagles Sunday Oliseh, ya ce daga Lionel Messi har Cristiano Ronaldo, babu wanda ya yi abunda za a kira shi dan wasan da ba a taba irinsa ba a duniya.
A maimakon haka Oliseh ya ce yana da yakinin cewa tun daga Diego Maradona har Messi da Ronaldo, babu wanda ya kamo Pele a matsayin shahararren dan kwallo da duniya ta taba gani.
Baya ga lashe kofin duniya sau uku a zamaninsa, Pele na Brazil ya zamo allon kwaikwayo ga matasan yan kwallon da suka yi nasara a wannan zamani.
Asalin hoton, OTHER
Da aka tambaye shi ko wa yake gani a matsayin dan kwallon da ba bu irinsa a duniya? Oliseh bai bata lokaci ba ya kada baki yace ” sunan shi Pele.”
” Shi ne dan wasan da duniya ba ta taba ganin irinsa ba har yanzu. Ba zai yiwu ka lashe kofin duniya ba har sau uku, a ce ga wani yana gasa da kai.”
”Na san wasu musamman matasa, ba za su ji dadin zabi na ba, amma ire-ire na da muka girme su mun san ko wane ne shi.” In ji Oliseh.
To amma dan wasan gaban PSG Lionel Messi, ya nuna kansa a matsayin daya daga cikin shahararrun yan kwallo a duniya, bayan da ya taimaka wa kasarsa Argentina lashe kofin duniya na 2022 a Qatar.