Ba Buhari ne ke Mulkin Najeriya ba –  Naja’atu Bala


Aisha Ta Fadi Gaskiya Na Cewa Ba Buhari

Ne Ke Mulkin Nijeriya Ba, Inji Hajiya Naja’atu
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa mutum biyu ke mulkin Nijeriya, Kawunsa Mamman Daura, da shugaban ma’aikata na fadar Gwamanatin Aso Rock Abba kyari, su ke mulkin kasar nan, ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Naja’atu Bala ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilin gidan Rediyon Amurka, da safiyar yau Juma’a.
Ta kara da cewa, Mamman Daura shi ya kawo Abba Kyari, Buhari ya ba shi mukamin shugaban ma’aikata na fadar Gwamnati, amma Buhari ya na iya bada ummarnin a yi abu, Kyari ya hana.
Dr. Naja’atu  Bala ta kara da cewa Mamman Daura da Kyari sune ke mulkin kasar nan a halin yanzu ba Buhari ba, don haka maganganu matarsa A’isha gaskiya ta fada, ya kuma zama dole a gyara.

You may also like