Ba Gaskiya Bane Batun Cewa Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Kasar Amurka Gobe Ba baskiya bane cewar wai shugaba Muhammadu Buhari ya shirya tsaf zuwa kasar Amurka bisa gayyatar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa, kamar yadda Lauretta Onuchie mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen sadarwa ta zamani ta bayyana. 
“Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne wanda a koda yaushe yake sanar da ‘yan Nijeriya dukkanin tafiye tafiyensa koda kuwa a cikin kasa Nijeriya  ne . Mutum ne mai matukar daraja ‘yan Nijeriya, ba zai taba yiyuwa ba ya saci hanya ya bar kasar nan ba tare da sanar da wadanda suka zabe shi ba domin ya yi musu aiki ba”.

You may also like