Ba Ja Da Baya Kan Aiwatar Da Dokar Hana Kiwo – Gwamnan Taraba


Gwamnan Taraba, Darius Ishaku ya jaddada cewa ba ja da baya a shirin da gwamnatinsa ke yi na aiwatar da dokar hana kiwo da kuma kafa wuraren kiwo na musamman a jihar.

Gwamnan ya ce, gwamnati ta jinkirta aiwatar da shirin dokar ne don ganin ba a muzgunawa jama’a ba inda ya ce gwamnatin jihar ta yi kokari wajen yaki da barayin Shanu. Ana dai ci gaba da tafka kazamin rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

You may also like