Ba Lalle Rashin Lafiyar Tinubu Ne Ya Sa Aka Dage Fara Kamfen Din APC Ba-Barayan Bauchi
Babban daraktan kamfen din gwamnan Filato Simom Lalong ya ce an dage kamfen din ne don fadada jerin sunayen wadanda za a shigar wajen jagorancin kamfen.

Bayanan na Lalong sun kara haifar da tambayar wane irin jerin sunaye ne bayan wanda a ka gabatar da ya hada da gwamnoni har ma shugaba Buhari ya ba da umurnin zare sunan mataimakinsa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnati Boss Mustapha don su maida hankali ga sha’anin gwamnati.

Yayin da ya ke tabbatar da Tinubu ya fice daga kasar da tawaga zuwa ketare ko ma a ce London, jigon kamfen din Barayan Bauchi, Sunusi Baban Takko, ya ce kowa na iya kamuwa da rashin lafiya a irin shekarun Tinubu amma lafiyar kalau ya fice daga kasar.

Tsohon mataimakin takarar Tinubu Ibrahim Masari da ke magana daga London ya ce ba sa haufin shiga kamfen din da kuma jin su na da tagomashin lashe zabe.

Tuni dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya shirya kaddamar da kamfe a farkon Larabar nan da ta ke ranar fara kamfen a hukumance.

Ga rahoton a sauti:

You may also like