Ba mu biya Boko Haram kudi ba kafin sako yan matan sakandaren Dapchi – Lai Muhammad


Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya ce gwamnatin tarayya ba ta bawa yan kungiyar Boko Haram kudi ba kafin su sako yan matan sakandaren Dapchi.

Muhammad ya bayyana haka ya yin da yake magana da yan jarida dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya amince cewa gwamnati ta tattauna da kungiyar inda aka da cewa babu batun rikici ko kuma farma juna.

Ministan ya ce yan ta’addar sun amince su dawo da yaran garin inda suka dauke su.

 “An saki yan matan ba tare da wani sharadi ba, babu kudin da aka bayar,  su (Boko Haram) sun bada sharadi daya cewa za su dawo da yan matan inda suka dauke su. Saboda haka da safiyar yau sun dawo da yan matan kuma yawancinsu sun tafi gidan iyayensu,”ya ce 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like