Ba Mu da BuKatar Sake Yi wa Obasanjo Raddi – fadar Shugaban Kasa


Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa ba za ta yi raddi ga Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo bisa sake kiran da ya yi ga ‘yan Nijeriya kan kada su kuskura su sake zaben Shugaba Buhari.

A cewar Fadar Shugaban kasa, amsar wasikar da tsohon Shugaban ya rubutawa Buhari kwanaki wanda Ministan Yada Labarai ya bashi ya wadatar kuma an nada Buhari a matsayin Ministan mai a zamanin mulkin soja na Obasonjo don haka babu bukatar yin musayar kalamai da tsohon Shugaban.

You may also like