Shugaban Kamfanin Mai na Kasa(NNPC) Maikanti Baru ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa gwamnati ba ta da wani shiri na kara farashin man fetur a yanzu.
Shugaban ya bayyana hakanne ne bayan wasu rahotanni da ke cewa manyan dillalan mai sun koka da karancin kudaden waje wanda suke amfani da su wajen sayo tataccen mai daga kasashen waje.
Maikanti, ya kara da cewa kamfanin NNPC ya tanadi wadataccen mai har kusan lita Bilyan 1.4 wanda ‘yan kasar za su amfana da shi kuma gwamnati ta riga ta tanadi kudaden waje domin sayo mai.