Kungiyar ‘yan uwa Musulmi, almajiran shaikh Ibrahim Zakzaky ta mabiya Shi’a, ‘Islamic Mobement in Nigeria’ ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin Malamin nasu domin su samu damar kai shi kasar waje don neman maganin raunukan da sojoji suka ji masa a rikicin da ya auku tsakaninsu da Sojojin a watanin baya.
Shugaban dandalin Resource Forum na kungiyar, Farfesa Abdullahi Danladi ne ya yi wannan kira a wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna cikin makon da ya gabata domin bayyana irin halin da Malamin nasu ke ciki a halin yanzu, wanda iyalansa suka ziyarce shi, kuma suka taras da shi yana fama da jiki.
“Shaikh Ibrahim Zakzaky na da damar neman magani a kasar waje a matsayinsa na dan Nijeriya. Idan Shugaba Buhari zai je kasar waje neman magani saboda Nijeriya babu kayan kiwon lafiya ingantattu, babu dalilin da za a hana Malam Zakzaky neman magani a kasar waje,” In ji Farfesa Abdullahi.
Danladi ya ci gaba da cewa, Dan Malam Zakzaky, Muhammad ya rubuta takarda a makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa, kullum idanun Malamin suna kara dushewa ne, amma hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta ki amincewa da bukatar iyalan Malamin na neman magani a waje.
Haka kuma Farfesan ya bayyana cewa ci gaba da tsare Shaikh Ibrahim Zakzaky, abu ne wanda ya saba ma ka’ida, musamman a daidai wannan lokaci da rayuwarsa ke cikin mawiyacin hali. Inda ya karyata maganar da ake yi na cewa wai Malamin da matarsa na cikin koshin lafiya. Ya ce a halin da ake ciki, idan har ba a dauki matakin gaggawa ba, to Malamin na iya rasa idanunsa gaba daya. Saboda haka sai ya ce, maganar cewa Malamin na cikin koshin lafiya, wannan ba gaskiya ba ne.
“Maganar da gwamnati da jami’an tsaro ke yi na cewa wai zuwa yanzu sun kashe kudi har sama da Naira Miliyan Biyar wajen inganta rayuwar Malam, da samar masa abubuwan more rayuwa, da abinci mai inganci, wannan ba gaskiya ba ne, saboda shaidu da ido sun bayyana cewa Malam da mai dakinsa na cikin wani mawiyacin hali, “ in ji shi.
Ya ci gaba da bayyana wa manema labaran cewa, “tun bayan da aka tsare Malam, yau kimanin watanni takwas ke nan, sau hudu kawai jami’an tsaro suka bari iyalansa suka sami damar zuwa su duba lafiyarsa, duk da kasancewa har yanzu gwamnati da jami’an tsaron sun ki yarda a ba kwararrun Likitoci damar zuwa su duba lafiyarsa. Domin ko kwanan nan sai da daya daga cikin ‘ya’yan Shaikh Zakzaky, wanda shi kadai ne dansa na namiji wanda ke raye, ya bayyana cewa ko wane lokaci daga yanzu, mahaifin nasu na iya rasa idanunsa gaba daya, musamman a sakamakon munanan raunuka da ya samu a fuskarsa, sannan akwai raunuka a jikinsa.”
“A bangare daya kuma, har yanzu akwai sauran raunin harbin harshashi a jikin Malam, wanda tun bayan harbin da jami’an sojoji suka yi masa a cikin gidansa, yau kimanin watanin takwas ke nan, amma har yanzu Likitoci sun kasa yin komai akan lamarin lafiyarsa. Hatta shi kansa babban Likitan da DSS suka dauka domin ya duba lafiyar Malam, ya shaida wa Malam cewa, gaskiya har idan ba a dauki matakin gaggawa ta hanyar hada gwiwa da wasu kwararru Likitocin ido ba, to tabbas babu makawa Malam na iya rasa idanuwansa gaba daya,” in ji shi.
Kungiyar ta IMN ta kuma kara bayyana cewa, hatta ita ma matar ta Shaikh Ibrahim Zakzaky, wato Hajiya Zeenatu tana cikin mawiyacin hali, domin a maganar da ake yi yanzu akwai harshashi a cikin gadon bayanta wanda ba a cire ba, wanda suka ce in har ba a yi da gaske ba, hakan na iya haifar mata da nakasar rasa wani sashe na jikinta.
Saboda haka sai suka bayyana cewa, “tabbas mun damu matuka da yadda ake ci gaba da tsare Malam ba bisa ka’ida ba, kuma har yanzu gwamnati ta kasa bayyana laifi daya da ta kama Malam da shi. Har yanzu gwamnati ta kasa gabatar da Malam a kotu domin sauraron irin laifukan da ake zarginsa da su. Tabbas ci gaba da yin hakan ba karamin zalunci da tauye hakkin dan adam ba ne. Tabbas ci gaba da tsare Malam ya saba ma tsarin mulkin dokar kasar nan.”
Daga karshe kungiyar ta IMN ta bukaci ci gaba da samun goyon bayan kungiyoyin kare hakkin dan adam, kungiyar ‘yan jaridu da dai sauran kungiyoyin sa-kai domin ganin sun ci gaba da nuna adawarsu da ci gaba da tsare Malamin da ake yi ba bisa ka’ida ba, har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halin ta.