
Asalin hoton, Getty Images
Wakilin dan kwallon nan dan kasar Ghana mai suna Christian Atsu ya ce ba a san inda dan kwallon yake ba, kwana guda bayan da rahotanni suka ce an ceto shi daga baraguzan wani gini, inda aka ce “ya sami raunuka” bayan girgizar kasar da ta auku a Turkiyya.
Dan wasan gaban na buga wa kungiyar Hatayspor ta Turkiyya kuma mataimakin shugaban kungiyar Mustafa Özat ya ce an ceto dan kwallon.
“Muna yin duk mai yiwuwa domin gano inda Vhristian yake”, inji Nana Sechere.
A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, wakilin dan wasan ya ce: “Bayan mun sami bayanai daga kungiyar Christian cewa an ceto shi da rana, har yanzu ba mu sami tabbacin inda yake ba.”
‘Akwai rudani’ kan inda Atsu yake
Shugaban kungiyar Hatayspor Volkan Demirel ya shaida wa shafin intanet na Spor Arena cewa babu labari kan inda Atsu ko inda daraktan wasanni Taner Savut, wanda shi ma tun ranar Litinin aka sanar da ba a san inda yake ba.
Har zuwa wannan lokacin ba a san halin da Savut ke ciki ba.
Jakadar Ghana a Turkiyya, Francisca Ashietey-Odunton ta shaida wa tashar rediyon kasar Joy FM cewa “akwai rudani” kan inda aka tafi da Atsu.
“Jiya, ma’aikatar harkokin waje a nan ta shaida min cewa tana son tabbatar da ko an ceto Christian Atsu, ko kuma an kai shi wata cibiyar kiwon lafiya” inji ta.
“A yau kuma sai ma’aikatar harkokin wajen ta shaida min cewa jami’ai na kokarin gano inda aka kai shi, kuma za a sanar da ni abin da suka gano nan ba da dade wa ba.”
Atsu dan wasa mai shekara 31 ya buga wa Newcastle wasanni 107, kuma ya buga wasa a Chelsea da Everton da kuma Bournemouth.
Ya kuma buga wa Ghana wasanni 65 daga baya kuma ya koma kungiyar Hatayspor a watan Satumba bayan ya bar kungiyar Al-Raed ta Saudiyya.