
Asalin hoton, FACEBOOK/NASIRU GAWUNA
Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC mako daya ta sake nazari kan sakamakon zaben gwamna na jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
APC ta bayyana haka ne a taron manema labaran da ta yi yau Talata inda ta bakin lauyanta na jiha, Barista Abdul Fagge ta ce baturen zaben ya yi kuskuren fahimtar dokar zabe wajen banbance sokewa sakamakon wasu wurare da aka yi sanadin tashin hankali da kuma zabe fiye da kima.
APC dai ta ce sam ba ta yadda da hanyar da aka bi wajen sanar da sakamakon zaben ba har aka bayyana Abba Kabir a matsayin zababben gwamna a don haka ta nemi a gaggauta sake yin zagaye na biyu na zaben.
Sai dai a cewar lauyan, baturen zaben ya yi la’akari ne kawai da batun tashin hankali wajen kare tazarar da ke tsakanin yan takara biyu – Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasir Gawuna na APC.
A ranar Litinin ne babban jami’in tattarawa da sanar da sakamakon zaben gwamna na jihar Kano, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda lashe zaben a don haka ya bayyana shi zababben gwamnan Kano.
Barista Fagge ya ce an karbi katunan zabe 273,442 a yankunan da aka soke zabe saboda matsalar tashin hankali da kuma yin zabe fiye da kima, adadin da ya ce na nufin ratar kuri’i 128,897 ba su kai a ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya yi nasara ba.
A na shi bangaren, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhasan Ado Doguwa ya bayyana cewa Inec ta sauka daga kan layin ka’idojin da ta yi amfani da su wajen ayyana zaben yan majalisar dokoki a yankinsa a matsayin wanda bai kammala ba.
Shi ma, dan takarar APC a jihar Nasir Yusuf Gawuna ya nemi magoya bayan jam’iyyar su ci gaba da kwantar da hankalinsu inda kuma ya bai wa iyalan wadanda aka kashe ko suka rasa dukiyoyinsu sakamakon tashin hankalin da aka yi a lokacin zabe da kuma bayan zaben hakuri.
Gawuna, wanda shi ne mataimakin gwamnan Kano ya bayyana fatansa cewa Inec za ta yi abin da ya dace ba tare da tauye ra’ayin galibin masu zabe ba a jihar.