Ba Musayar Fursunoni Muka Yi da ‘Yanmatan Chibok ba – Lai Muhammad


 

Gwamnatin Nijeriya ta musanta batun da ke zagaye a kafafen yada labarai na cewar ta yi musayar fursunoni ‘yan Boko Haram guda 4 ne domin sakin ‘Yan matan Chibok 21 daga cikin sama da 200 da aka yi garkuwa da su fiye da shekaru biyu suka wuce.

Wannan batu ya fito ne daga bakin Ministan yada labarai Lai Muhammad yayin da yake magana da manema labarai a Abuja.

Haka kuma shima mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adeshina, ya shaidawa jaridar RFI Hausa cewa babu wani musayar fursunoni da aka yi, kuma ba wasu kudaden fansa da aka biya ba domin ceto ‘yan mata na Chibok.

Dama dai a sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa an saki ‘yan matan ne sakamakon tattaunawar da ake tsakanin shugabannin kungiyar Boko haram din da gwamnatin Nijeriya yayin da kungiyar agaji ta duniya wato Red Cross tare da gwamnatin Switzerland suka shiga tsakani.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana wani cikakken bayani ba game da abun da ya sa aka saki ‘Yan matan, da kuma dalilin da ya sa aka saki guda 21 kawai.

Wannan magana dai ta sha bam bam da rahotannin da kafafan yada labarai suka wallafa da ke nuna cewa an yi musayar fursunoni ne da ‘yan matan. Kafar yada labarai ta BBC ta rahoto cewa wani jami’in tsaro ya shaida mata cewa tabbas musayar fursunonin aka yi.

chibok-girls

Tuni dai ‘yan matan suka isa fadar shugaban kasa da ke Abuja kuma suka samu tarba a hannun mataimakin shugaban farfesa Yemi Osinbajo. Ga sunayen ‘yan matan kamar yadda aka fitar:

Maryam Usman
2. Jummai John
3. Blessing Abana
4. Lugwu Sanda
5. Comfort Habila
6. Maryam Basheer
7. Comfort Amos
8. Glory Mainta
9. Saratu Emmanuel
10. Deborah Ja’afaru
11. Rahap Ibrahim
12. Helen Musa
13. MaryamLawal
14. Rebecca Ibrahim
15. Asabe Goni
16. Deborah Andraus
17. Agnes Gabani
18. Saratu Marcus
19. Glory Damma
20. Binda Nuhu
21. Rebecca Malo

You may also like