Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe a ranar Asabar yace bazai aje Mulkinsa ba, yace ba mutuwa zanyi ba duk da nakai Shekaru 93 a duniya.
Shugaba Robert Mugabe yana Mulkin kasar tun 1980 lokacin da suka samu ‘yancin Kansu.
Rashin lafiyar Robert Mugabe ya tashi hankalin dubbannin ‘Yan kasar yayinda Mutanen Kasar sukayi dandazo a garin Chinhoyi Gidan Robert Mugabe likitoci sunyi mamaki da karfin qashin bayansa.
Yace anata jita-jitar zan aje Mulki, zan mutu yana bazuwa a gari Toh bazan Aje Mulki ba.
Mugabe yayi tafiya kadan-kadan a wajen taron ba tare da Dan jagora ba.