Umma Shehu ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da sashin Hausa na BBC yayi da Ita, na tsani gulmace gulmace da gutsuri tsoma a rayuwata, inji ta.
Tauruwar na ganin ya kamata mata su tashi tsaye su zama masu shiryawa da bada umarni da daukar nauyin fina-finan Hausa maimakon su tsaya a ringa sa su a fim.
Umma Shehu wacce ta shafe shekara uku a Kannywood ta ce babu wani kalubale da ta ke fuskanta a harkar fim din, wacce ta ce ta dauke ta a matsayin babbar sana’a.
” Bani da Saurayi a Hausa Film sai abokin aiki, sannan bani da Kawa a Industri sai Abokiyar aiki ” Inji jarumar