Ba Ni da Niyyar Komawa Nollywood – Rahama Sadau


 

A wata hira da ta yi da jaridar Premium Times, Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa ba ta da niyyar komawa ma’aikatar shirya fina-finai na turanci wato Nollywood a sakamakon korarta da aka yi daga Kannywood.

Jarumar ta ce yunkurinta shi ne ta ga ta raba kafa tsakanin ma’aikatun guda biyu domin a fadarta, babu banbanci da yawa tsakanin Nollywood da Kannywood illa na al’adu wadanda aka dauka da matukar muhimmanci.

Haka kuma jarumar ta jaddada cewa akwai iyakun da ta sanyawa kanta da baza ta taba tsallakawa ba, ta ce ko ana so ka ba’a so ita ‘yar Arewa ce kuma yawancin masoyanta a arewa suke, a don haka ba za ta so ta yi wani da zai sa su juya mata baya ba.

Tun da dai aka kori jarumar daga Kannywood makonni biyu da suka wuce ne wasu daga cikin masoyanta ke ganin zai fi mata kyau idan ta koma Nollywood.

You may also like