Ba ruwan addini da yakin da ake a duniya- Fafaroma


 

Fafaroma Francis ya ce duniya na cikin yaki a halin yanzu amma babu ruwan addini da kashe kashen da ake yi a kasashen duniya. Shugaban mabiya darikar Katolika ya fadi haka a ziyarar da ya kai Poland bayan kisan wani Malamin katolika a Faransa.

A cikin jawabinsa da ya gabatar a birnin Krakow na Poland Fafaroma ya ce hanyar da za a magance tsoro da fargaba shi ne amincewa da mutanen da ke kauracewa yaki ko rikici a kasashensu.

Shugaban na mabiya darikar katolikan ya fadi haka ne bayan kisan wani malamin katolika a Faransa.

Fafaroma ya ce bude kofa ga ‘yan gudun hijira babbar hikima ce da nuna tausayi tare da danganta ukubar da ‘yan gudun hijira suka fuskanta bayan wasu gwamnatoci sun ki amincewa da su a zamanin yakin duniya na 11.

Fafaroma ya ce babu ruwan addini da yaki, domin dukkanin addinai na da’awa ne akan zaman lafiya.

Ya ce ana yaki ne kawai saboda bukatun wasu don neman kudi ko dukiya amma ba don addini ba.

A ranar Talata ne dai aka kashe Malamin na katolika a Faransa, amma Fafaroma ya ce an kashe dubbai da kananan yara kafin shi.

You may also like