Ba Wanda Ya Isa Ya Hanani Shiga Fadar Shugaban Ƙasa – El-Rufa’i Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i a jiya Juma’a ya gudanar da sallar Juma’a tare da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a masallacin Juma’a dake fadar ta Aso Villa. 

Bayan idar da sallar ne Gwamna Elrufai ya bi tawagar shugaba Buhari zuwa gurin karɓar baki dake ofishin, inda suka tattauna tare da Shugaban kasa. 

Jim kaɗan da kammala tattaunawar Gwamna Rufa’i ya gana da manema labarai dake gidan Gwamnati, inda ya shaida musu cewa babu wanda ya isa ya hana shi shiga Villa.

Wannan martani ba ya rasa nasaba da wata wasiƙa da El- Rufa’in ya rubuta wa shugaba Buhari. Amma daga bisani wasikar ya karade kafafen jaridu. Inda Gwamnan na Kaduna ya furta cewa wadanda ya rubuta wasikar akan su ne suka fito da ita don su bata masa suna. 

You may also like