Ba Wanda Ya Isa Ya Kaiwa Kabilar Igbo Hari A Jihar Neja – Cewar Gwamna Abubakar Sani BelloGwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yayi gargadi akan kaiwa ‘yan kabilar Ibo ko wata kabila hari a cikin Jihar Neja, domin Jihar Neja ta kowani dan Nijeriya ne.

A wata takardan sanarwa dake dauke da sanannun sakataren yada labaran gwamnan Malam Jibril Baba Ndace, Abubakar Sani Bello ya baiyana cewar hakkin gwamnatin Jihar Neja ne ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ta batare da nuna wariya ko sun zuciya ba.

Ya kara da cewar jami’an tsaron Jihar mu sun gaggauta baza  jami’an su a fadin Jihar musamman a wuraren da ake da fargabar barkewar rikici ta yadda za’a dakile duk wani yunkuri na haifar da tashin hankali a cikin Jihar Neja.

“Gwamnatin Jihar Neja bazata dunkule hannunta ta zura ido wasu baragurbin mutane marasa son zaman lafiya su haifar da rudani da tashin hankali tare da zaman fargaba a cikin al’umma ba.

Al’ummar Jihar Neja mutane ne masu son zaman lafiya  da marhabin da dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da banbancin yanki ko kabilar da suka fito ba, saboda haka duk wadanda aka kama da yunkurin haifar da tashin hankali a cikin al’ummar mu domin su samu damar lalata kaiyaki da satan dukiyoyin mutane zasu fuskanci tsatstsauran hukunci domin haline irin na ‘yan ta’adda.

Jihar Neja cibiyace ta tsakiyar Najeriya wacce a kowani rana take cigaba da karbar baki daga sassa daban daban, wasu daga cikin hamshakan mutane da tarihin Najeriya ba zai taba mantawa dasu ba daga kabilar ibo ‘yan Jihar Neja ne misali irin su: Chief Nnamdi Azikwe, Owole na Onitsha, Chief Odumegwu Ojukwu duk a garin Zungeru dake Jihar Neja aka haifesu.-Cewar Gwamnan.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Neja da karda su dauki doka ahannun su sakamakon rikicin dake faruwa a yankin kudu masu gabashin Najeriya, amma su kasance masu bin doka da oda na kasa, tareda cigaba da harkarkokin kasuwancin su, yakuma bada tabbacin zasu kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar.

“Ina kara tunatar da al’ummar Jihar Neja da ku kasance masu sanya ido akan al’amuran dake wakana a yankunan ku, tare da baiwa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wanda kuka ga yana yunkurin aikata aiyukan da suka sabawa doka ko wanda ke kokarin haifar da rikici a cikin al’umma- Inji gwamnan Neja.

Daga karshe gwamnan ya roki ‘yan kasa da su yi watsi dakarairayin da labaran kanzon kurege da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani akan wannan rikici.

You may also like